Labaran Kano
Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan shari’ar Ganduje da Abba
Kotun sauraran kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta tsayar da jibi Laraba a matsayin ranar ta karshe da zata yanke hukuncin wanda ya samu nasarar zaben gwamnan da aka yi a ranar 9 ga watan Maris da ya gabata, wanda dan takarar jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ke kalubalantar gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda ya lashe zaben gwamnan.
Kotun ta ayyana ranar ce ta hanyar aikawa dukkanin jami’un biyu sako ta hanyar wayar salula, wanda sakataren kotun ya aike musu.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar, a ranar 18 Satumba da ta gabata ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da jam’iyyar APC da gwamna Ganduje suka rubuta jawaban su na karshe yayin da dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya amince da rubuta jawabin karshen
Mai jagorantar shari’a mai shari’a Halima Shamaki ta ce kotun tana sane da adadin wa’adin kwanakin da aka ware mata na kwanaki 180, kamar yadda yake a cikin kudin tsarin hukumar INEC na tabbatar da ta yanke hukuncin kararrakin zabe cikin kwanaki 180 bayan da aka shigar da kara gabanta.
A yayin da suke gabatar da hujojin su lauyoyi masu kare bangaren da ake kara ,Ofiong Ofiong mai darajar SAN, da Alex Ezinyon da Ahmed Raji mai darajar SAN dukkanin su sun nemi da kotun ta kore karar suna mai cewar lauyan masu kara ya gazza gamsar da kotu shaidun da ake bukata ba, bayan da yayi ikirarin cewar, an tafka magudi a yayin zaben.