Connect with us

Labarai

Kotu ta yankewa wani matashi hukuncin kisa a Zamfara

Published

on

Babbar kotun jiha ta daya dake birnin Gusau na jihar Zamfara ta yankewa wani matashi mai suna Kamalu Yusuf mazaunin unguwar Geji dake Gusau hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Tunda farko dai ‘yan sanda ne suka gabatar da wanda ake zargi a gaban kotun bisa tuhumar aikata laifukan hada baki wajen aikata fashi da makami da kuma hallaka mahaifiyarsa Hajiya Hafsat Muhammad da kannensa Maryam Yusuf da Amina Yusuf har lahira a shekara 2013.

Wakilin mu a Zamfara Abdullahi Salisu Faru ya rawaito mana cewa ‘Yan sanda sun gurfanar da matashin Kamalu Yusuf tare da wani matashin mai suna Armaya’u Shehu, sai dai masu kara basu iya kawo kwararan shaidu akan shi Armaya’un ba.

Saboda haka ne babbar mai shari’a ta jihar Zamfara Hajiya Kulu Aliyu Gusau wadda ta jagoranci shari’ar ta sallami Armaya’un sannan ta yankewa Kamalu Yusuf hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da aka sameshi dumu-dumu da hannu wajen aikata laifukan.

Karin labarai:

Rahoto: Kan dalilan da ya sanya ake yawan samu kisan kai a tsakanin ma’urata

Kotu ta yankewa matashi hukuncin kisa a Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 328,299 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!