Connect with us

Labarai

Hukumar FRSC ta fara shirin daukar ma’aikata

Published

on

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa, FRSC, ta ce, za ta fara daukar ma’aikata na shekarata 2026 don ciki guraben da dama a hukumar wanda dama ce ga yan kasa.

Wannan na cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai sanye da sa hannun Mataimakiyar Shugabar Hukumar mai kula da harkokin gudanarwa  Pauline Olaye.

Ta cikin sanarwar, hukumar ta ce, ana neman cike gurabe daban-daban domin kara karfin hukumar  da nufin inganta ayyukanta a fadin kasar nan.

Hukumar ta bayyana cewa ana neman masu neman aiki a gurabe da dama  daga ciki kuwa akwai Assistant Route Commander da kuma Marshal Inspector na biyu da na uku, tare da Road Marshal Assistant na daya, na biyu da na uku.

Hukumar ta kuma ce, masu neman mukaman jami’ai dole ne su kasance sun kammala jami’a ko kuma kwaleji ko cibiyoyin da gwamnati ta amince da su, yayin da masu neman sauran mukamai za su cika sharuddan ilimi da kwarewar da aka tanada ga kowane rukuni.

Hukumar ta kuma ce masu sana’o’i da direbobi za su iya neman aiki a karkashin sashin Road Marshal Assistant.

Ta kara da cewa dole ne mai neman aiki ya kasance dan Najeriya kuma  ya iya amfani da kwamfuta, kuma ya kasance cikin koshin lafiya sannan a tanadi lasisin tuki da sauran abubuwan da aka bukata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!