Connect with us

Labarai

Kotu ta yi barazanar daure shugaban INEC Amupitan

Published

on

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta gargadi shugaban hukumar zaɓen ta kasa INEC, Farfesa Joash Amupitan, da sakataren jam’iyyar PDP, Sanata Samuel Anyanwu, kan yiwuwar dauresu idan suka gaza bin umarnin kotu.

 

Jaridar Punch ta rawaito cewa kotun ta fitar da sanarwa, inda ta jaddada hukuncin da ta yanke tun ranar 12 ga Janairu, wanda ya kori Anyanwu daga jam’iyyar PDP, kamar yadda aka tabbatar.

 

Kotun ta bayyana cewa idan Anyanwu da shugabannin INEC suka ci gaba da kin bin wannan hukunci, za a iya tuhumar su da raina kotu, wanda zai iya kai su ga dauri zuwa kurkuku.

 

Hakan na zuwa ne yayin da ake fama da rikicin shugabanci a PDP, wanda ya raba jam’iyyar gida biyu masu takaddama kan halaccin shugabanci.

 

A gefe guda, bangaren jam’iyyar da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta ya bukaci INEC da ta daina amincewa da Anyanwu a matsayin sakataren PDP, yana mai cewa tun bayan korarsa, ba shi da hurumin wakiltar jam’iyyar

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!