Connect with us

Labarai

Bauchi: Sojoji sun hallaka ’yan bindiga da dama tare da lalata maboyar su

Published

on

Dakarun Rundunar sojin Najeriya sun hallaka ’yan bindiga da dama tare da lalata maboyar su a Jihar Bauchi.

 

Gwamnan jihar Bala Mohammed Kauran Bauchi ne ya bayyana hakan bayan wani taron tsaro da aka gudanar a jiya Litinin.

 

Gwamnan ya bayyana cewa jami’an tsaro da haɗin gwiwa da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da kuma ’yan banga sun kai farmaki a dajin Malam da ya haɗa jihohin Bauchi, Filato da Taraba.

 

Yayin hare-haren an yi amfani da jiragen yaƙi guda huɗu, inda aka lalata sansanonin ’yan bindiga tare da kone baburan da suke amfani da su.

 

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!