Connect with us

Labarai

Ana yunƙurin yiwa ‘yan Najeriya kutse a bankunansu – CBN

Published

on

Babban bankin Najeriya CBN ya gargaɗi ‘yan ƙasar da su kasance cikin shiri saboda masu kutsen Intanet da ke ta yunƙurin kutse cikin asusun ɗaiɗaikun mutane.

Babban bankin ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hannun muƙaddashiyar harkokin watsa labarai Hakama Sidi Ali a ranar Talata.

CBN ya ce masu kutse na tura wani saƙo na bogi zuwa ga email ko sakon karta kwana na mutane suna cewa daga bankin sakon yake.

A cewa sanarwar akwai cutar da mutane a saƙon inda suke neman mutum ya danna wani link daga nan kuma sai su samu damar shiga cikin asusun.

Daga nan kuma sai su bar me asusun da zargin CBN ya sace masa kudi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!