Labarai
Fadar Sarkin Musulmi ta ƙaryata yin zanga-zangar ƙyamar shugaba Tinubu

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta ƙaryata labarin da ake yaɗawa ta wani bidiyo a shafukan sada zumunta inda ake cewa an gudanar da zanga-zangar ƙyamar shugaba Bola Ahmed Tinubu, a gaban fadar Sarkin Musulmin da ke Sokoto.
Majakisar Sarkin Musulmin ta ce batun zanga-zangar kirkirar sa aka yi ta hanyar amfani da wani tsohon bidiyo da aka naɗa shekaru kusan biyar da suka gabata.
You must be logged in to post a comment Login