Labarai
Aisha Binani ta janye karar da ta shigar a babbar kotun tarayya
A yau Laraba ne ‘yar takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Adamawa, Sanata Aisha Dahiru Ahmed, wadda aka fi sani da Binani, ta janye karar da ta shigar a kan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.
Rahotonni sun bayyana cewa tun farko ‘yar takarar ta jam’iyyar APC ta roki kotu da ta duba hukuncin da hukumar zabe ta INEC ta yanke na sauya bayyana ta tun farko a matsayin wadda ta lashe zabekamar yadda kwamishinan zabe na jihar Hudu Yunusa-Ari ya bayyana.
Lauyan Binani, Mohammed Sheriff, ya shaida wa mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa an bayar da sanarwar dakatar da hakan inda ya bukaci kotun ta yi watsi da karar.
Mai shari’a Ekwo ya tunatar da Sheriff cewa, an bayar da umarni a ranar da aka dage zaman da ya gabata inda aka umurce shi da ya yi magana a kotu kan ko kotu na da hurumin sauraren karar ko a’a.
Lauyan wanda ya shaida wa kotun cewa al’amura da dama sun faru tsakanin ranar da aka dage sauraren karar zuwa zaman kotun na yau, don haka ya roki kotun ta amince da janye karar.
You must be logged in to post a comment Login