Labaran Kano
Kotu ta yi watsi da karar Sarkin Kano mai murabus – Muhammad Adamu
Babban Sufeto ‘yan-sandan kasar nan Muhammad Adamu ya bukaci babbar kotun tarraya da ke zaman ta a birnin tarraya Abuja, da ta yi watsi da karar da Sarkin kano mai murabus Muhammdu Sunusi ya shigar gabanta, na hana shi shigowa jihar Kano.
A cewar Adamu, kotun ba ta da hurumin sauraren karar da Sarki mai murabus ya shigar gabanta.
Babban sufeton yan sandan kasar nan ya bayyana hakan ne ya yin, zantawa da manema labarai a birnin tarraya Abuja.
A cewar sa, kotun ta dakatar da karar ba tare da ba ta lokaci ba, zuwa wani lokacin.
Tun a ranar tara ga watan Maris wannan shekara ne dai, gwamnatin jihar Kano ta sauke Muhammad Sunusi daga kan karagal mulki.
You must be logged in to post a comment Login