Connect with us

Labarai

An gargadi ‘yan Najeriya da ke Afirka ta kudu kan zanga-zangar kasar

Published

on

Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje NiDCOM ta bukaci ‘yan kasarnan da ke zaune a Afrika ta Kudu su bi umarnin da ofishin jakadancin Najeriya ya bayar, sakamakon zanga-zangar kyamar bakin haure da ta barke a wasu yankuna na kasar.

Rahoton ya ce rikice-rikicen sun faru a biranen East London, Cape Town, Durban da KwaZulu-Natal, inda aka samu sace-sace, lalata kadarori da raunata mutane. 

Haka kuma an shirya sabbin zanga-zanga a Gauteng daga 27 zuwa 29 ga Afrilu, 2026, domin matsa wa gwamnatin kasar lamba kan domin korar baki a kasar.

Hukumar ta ce karamar Ministar Harkokin Wajen kasar nan, Ambassador Bianca Ojukwu, tana tattaunawa da jami’an gwamnatin Africa ta Kudu domin shawo kan matsalar. 

Ta kuma bukaci ‘yan Najeriya su kasance masu bin doka tare da kauce wa wuraren da ake hargitsi.   

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!