Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Kotu ta umarci a sake shari’ar matashin da ake zargi da ɓatanci ga Musulunci

Published

on

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Kano ƙarƙashin mai shari’a Nasir Saminu da babban jojin Kano sun bada umarnin komawa domin a sake shari’ar matashin da aka yanke wa hukuncin kisa.

A zaman Kotun na Alhamis mai shari’a Nasir Saminu ya ce, akwai kura-kurai a cikin shari’ar da aka yi masa a baya.

Mai shari’ar ya ce, an samu rashin shawarwari daga wajen lauyoyin wanda ake tuhuma.

A baya dai wata kotun shari’ar Musulunci ce ta yanke wa matashin Yahya Aminu Sharif hukuncin kisa bisa samunsa da laifin yin ɓatanci ga fiyayyen halitta (s.a.w).

Muna tafe da ci gaban labarin a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!