Labarai
Kotun ɗa’ar ma’aikata ta sanya ranar da za ta yanke hukunci tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar NARD
Kotun ɗa’ar ma’aikata ta ƙasa ta saka ranar jumma’a 17 ga watan Satumba a matsayin ranar da zata yanke hukuncin ƙarar da gwamnatin tarayya ta kai ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa.
Ƙarar dai ta biyo bayan yajin aikin da ƙungiyar ke gudanarwa sama da wata guda.
Mai shari’a Bashar Alkali, ne ya saka ranar ne biyo bayan sauraron duka bangarori biyu da ƙorafin da suka shigar dangane da taƙaddamar da ta barke tsakanin su akan yajin aikin da ƙungiyar ta tafi, da kuma batun babu aiki babu biyan albashi.
Da yake gabatar da jawabi Alƙalin ya buƙaci bangarorin biyu da su zauna a teburun shawarwari don samun matsaya kafin komawa kotun.
You must be logged in to post a comment Login