Labarai
Kotun Kolin Brazil ta haramta Dan takarar shugaban kasar ziyartar mahaifinsa

Kotun Kolin kasar Brazil ta haramta wa dan takarar shugaban kasa, Flavio Bolsonaro, ziyartar mahaifinsa, tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro, na tsawon kwanaki 90.
Matakin ya biyo bayan da Kotun ta ce sun karya sharuddan da aka gindaya wa tsohon shugaban kasar na zaman gidan yari.
Alkalin kotun, Alexandre de Moraes, ne ya bayar da umarnin a jiya Litinin bayan Flavio ya karanta wata wasika da mahaifinsa ya rubuta da hannu yayin wani shirin kai tsaye (livestream) a kafafen sada zumunta.
You must be logged in to post a comment Login