Labarai
Majalisar Dattawan ta yi barazanar ladabtar da NCAA da SMEDAN da ITF

Majalisar Dattawan ta yi barazanar daukar matakin ladabtarwa kan Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa NCAA, hukumar bunkasa Kananan da matsakaitan masana’antu ta SMEDAN da Asusun horar da Ma’aikata na Masana’antu ITF saboda rashin amsa gayyatar kwamitinta da ke binciken yadda aka aiwatar da rangwamen harajin shigo da kayayyaki da ya kai naira tiriliyan 34.
Majalisar ta bayyana rashin gamsuwarta da yadda hukumomin suka gaza gabatar da bayanan da ake bukata domin tantance yadda aka gudanar da shirin rangwamen harajin.
Sanatocin sun ce idan hukumomin suka ci gaba da gaza ba da cikakken bayani, za su fuskanci matakan ladabtarwa kamar yadda doka ta tanada.
Majalisar ta kuma jaddada cewa manufarta ita ce tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma kare kuɗaɗen al’umma.
You must be logged in to post a comment Login