Labaran Wasanni
Kotun shari’ar wasanni ta CAS ta kori karar Wydad Athletic
Kotun shari’ar wasanni wato Court of Arbitration for Sport (CAS), ta yi watsi da karar da kungiyar Kwallon kafa ta Wydad Athletic Club , ta kasar Morocco ta shigar gabanta , na kalubalantar nasarar da aka baiwa Esperance a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Zakarun Afirka na CAF Champions league na shekarar 2019.
A baya kungiyar ta garzaya Kotun don sake neman a dawo a buga wasan don samun Zakara bayan da hukumar CAF ta baiwa Esperance Nasara sakamakon ficewa daga filin wasa da ‘yan tawagar Wydad suka yi bayan alkalin wasa ya hana Kwallon da suka farke ta hannun Walid El Karti , ana wasan da suka nemi Alkalin wasan da ya duba na’urar Bidiyo ta VAR.
Wasan dai a ba a samu damar cigaba da buga shi ba, sakamakon kin dawowar tasu wanda hakan yasa CAF ta baiwa tawagar Esperance Nasara kasancewar ita ke jagorantar wasan da ci 2-1.
Kotun ta CAS, ta aminta da hukuncin kwamitin karbar korafi na hukumar CAF , da ya baiwa tawagar Esperance Nasara ta zama Zakaran gasar , na shekarar 2018/19.
You must be logged in to post a comment Login