Labarai
Kowanne banki ya gabatar da kadarorin sa kafin watan Yuni – EFCC
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bukaci masu harkar hada-hadar kudi a Najeriya musamman masu bankuna da su bayyana kadarorinsu ga hukumar kafin wa’adin daya ga watan Yuni mai zuwa.
Shugaban Hukumar, Abdulrashed Bawa ne ya fadi wannan bayanin a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa jimmkadan bayan kammala ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugabn hukumar kan al’amuran yada labarai licity Wilson Uwujaren ya fitar, na bayyana cewa matakin ya biyo bayan tantance ayyukan ma’aikatan Banki da sauran al’amuran da suka shafi kudi karkashin dokar bayyana kadarori ta shekarar 1986.
A cewar sanarwar sashi na 1 na ma’aikatan Bankin da al’amuran kudi ta tilasta kowane ma’aikacin Banki da ya yi cikakken bayani game da kadarorin da ya mallaka lokacin aiki, da kuma duk shekara.
You must be logged in to post a comment Login