Connect with us

Labarai

KSCPC ta kama gurɓataccen Tumaturin gwangwani

Published

on

Hukumar kare haƙƙin masu sayen kaya ta jihar Kano KSCPC da haɗin gwiwar hukumar KAROTA sun cafke wata mota maƙare da gurɓataccen Tumaturin gwangwani.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:56 na daren Talata, a kasuwar Singa.

Mai taimakawa Gwamnan Kano kan KAROTA Malam Nasir Usman Na’ibawa wanda ke jagorantar sumamen ya ce, yawan Tumaturin da suka kama ya kai katan 368.

A cewar sa, gurɓatacce ne da wa’adin amfani da shi ya ƙare, saboda haka hukumomin za su ci gaba da bincike domin ɗaukar mataki na gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!