Labarai
KTPCACC ta fara bincike kan zargin karkatar da kuɗi da kayan gwamnati

Hukumar Karɓar Ƙorafi da yaki da din Hanci da rashawa ta jihar Katsina KTPCACC, ta fara bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗe da kayayyakin gwamnati a wasu makarantu da ma’aikatun gwamnati.
Hukumar ta ce ana binciken shugabannin makarantu huɗu da suka fito daga Danja da Rimaye da Maigora da kuma Kurami kan zargin karkatar da naira miliyan 6 da dubu ɗari shida da kuma siyar da kadarorin makarantu ba bisa ka’ida ba.
Haka kuma hukumar ta fara bincike kan zargin karkatar da naira miliyan 46 yayin rabon tallafin taki, da kuma naira miliyan 136 a Ma’aikatar Kuɗi ta jihar.
Hukumar ta ce, an riga an dawo da wani ɓangare na kuɗin, ragowar kuma ana ƙoƙarin dawo da su.
Sakataren hukumar, Jamilu Abdulsalam, ya ce, za su bi duk hanyoyin doka domin dawo da dukiyar jama’a.
You must be logged in to post a comment Login