Labarai
Kudaden da aka warewa fannin noma a kasafin bana yayi kadan- Farfesa Abba
Babban mashawarcin kungiyar gwamnoni Nijeriya a fannin noma Farfesa Abba Gambo, ya bayyana damuwa dangane da karancin kudaden da gwamnatin tarayya ta warewa ma’aikatar noma da samar da abinci a kasafin kudin bana.
Farfesa Abba Gambo ya ce kudin da aka warewa ma’aikatar na naira biliyan 110.25 bai kai ko kaso daya bisa dari na kasafin kudin bana na tiriliyan 28 ba, wadda tuni majalisun dokokin kasar suka amince da shi.
A cewar Farfesan, ‘kudaden da aka ware sun saba da yarjejeniyar da aka cimma a shekarar data gabata ta 2023 a Maputo, inda aka amince cewa kasashen Africa ciki har da Nijeriys zasu warewa fannin noma kaso goma cikin dari daga cikin kasafin kudaden su a kowacce shekara, domin samar da wadataccen abinci a nahiyar baki daya’.
Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin
You must be logged in to post a comment Login