Labarai
Kula da albashin ‘yan sandan al’umma ya rataya a wuyan jihohi – Rundunar ‘yan sanda
Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta ce nauyin kula da albashi da kuma ‘yan kunji-kunji na ‘yan sandan al’umma da gwamnati ke kokarin kirkirowa a kwanan nan, ya rataya ne a wuyar jihohin kasar nan.
Mukaddashin sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan mai kula da harkokin bincike na tsare-tsare, Adeleye Oyebade ne ya bayyana haka ya bayyana haka ta cikin wani shirin gidan talabijin na Channels mai taken: ‘Sunrise Daily’.
Ya ce, har gobe ‘yan sandan kasar nan za ta ci gaba da kasancewa guda daya dunkulalliya, ‘yan sandan al’umma da za a dauka za su rika aiki ne na wucin gadi.
DIG Adeleye Oyebade ya kuma ce ‘yan sandan na al’umma da za a dauka aiki zasu gudanar da aiki ne karkashin sashe na arba’in da tara da hamsin na dokokin rundunar ‘yan sandan kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login