Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An dakatar da wasan PSG na farko a gasar League 1

Published

on

Mahukuntan shirya gasar League 1 ta kasar Faransa ta dage wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain da za ta yi a wasan farkon gasar zuwa kwanaki 12 masu zuwa a nan gaba.

PSG za ta kara da Lens a ranar Asabar mai zuwa, amma an dage wasan ne sakamakon kungiyar PDG ta bukaci hakan domin ‘yan wasan ta su huta, sakamakon sun kammala wasan karshe da Bayern Munich a ranar Lahadin da ta gabata a kasar Portugal.

Yanzu haka kungiyar za ta fara wasan ta ne a ranar 10 ga watan Satumba a gasar ta League 1, bayan hutun kwanaki 12 da a ka bata.

An dai fara gudanar da gasar ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda a ka dakatar da wasan kungiyar ta PSG da Metz sakamakon wasan su na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai da suka fafata da kungiyar Bayern Munich a ranar Lahadin makon jiya.

PSG dai ta yi rashin nasarar daukar kofin gasar a hannun Bayern Munich da ci daya mai ban haushi a gasar ta cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!