Labarai
Kun san yau ake bikin ranar wanke hannu ta duniya?
An dai fara bikin ranar ne a shekarar 2008, don fadakar da al’umma mahimmancin da wanke hannu da sabulu ko sindarin da zai kashe kwayoyin cuta nan take.
Haka kuma ranar dama ce da ke nuni kan yadda za’a magance matsalolin yaduwar kananan cutuka da ake kamuwa da su ta hanyar amfani da hannu mara tsafta, tare kuma da bayyana irin illolin da rashin wanke hannu ke da shi a tsakanin al’umma.
Taken ranar a bana shi ne,’wankakken hannu ga kowa da kowa’, kuma taken ya biyo bayan bayyanawa al’umma irin hadarin da rashin wanke hannu yake da shi ta hanyar haifar da manya da kananan cututtuka da ka iya yin sanadiyyar rayuwar mutane masu yawa tare da da dakushe tattalin arziki da ci gaban al’umma.
Wasu mutane da Freedom Radiyo ta zanta da su a nan birnin Kano sun bayyana yadda suke kula da wanke hannayen na su, ta wajen amfani da sabulu da kuma Toka da dai sauran su.
Dr. Bashir Bala Getso na kwalejin koyon aikin tsafta ta nan Kano, ya bayyana cewa, wanke hannu na daya daga cikin hanyoyi masu saukin takaita yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma.
Dr. Aminu Bashir na sashen kula da lafiyar iyali dake asibitin koyarwa na Aminu Kano ya bayyana hanyoyin da za’a bi wajen wanke hannu musamman ma wajen amfrani da sinadaren kashe kwayoyin cuta.
Ya ce ta hanyar wanke hannu na taimakawa gaya wajen inganta lafiyar jama’a tare da rage asarar rayuka, sakamakon yaduwar manya da kananan cutuka masu saurin illata dan adam.
Taken ranar ta bana dai ya biyo bayan tunatarwa kan mahimmancin da wanke hannu ya ke da shi ta yadda al’umma za su taka muhimmiyar rawa wajen magance takaita yaduwar cutaka a tsakaninsu.
Ana gudanar da ranar wanke hannu ta duniya a duk ranar 15 ga watan oktobar ko wacce shekara, da nufin wayar da kan al’umma a kan muhimmancin wanke hannu a ko wanne lokaci.
Haka kuma, ranar na nuni kan yadda za a kawo karshen yaduwar cututtukan da ke da alaka da rashin tsaftace hannu.