Kiwon Lafiya
Kungiyar al’ummar Musulmin jihar Lagos ta bukaci Samar da kotun shari’ar mulsunci
Kugiyar al’ummar Musulmi da ke jihar Lagos ta buka ci da a samar da kotun shari’ar musulunici da za ta dinga shari’a kan al’amuran da suka shafi addinin musulunci.
Kugiyar na mika wannan bukata ne a lokacin da suke tattaunwa da dantakar Gwamnan jihar a jam’iyyar AD mista Owolabi Salis a jiya laraba.
A cewar kugiyar al’ummar musulmi na bukatar a gina musu kotun addinin musulunci, duba da cewa a yanzu haka al’amaran musulmi na hannun wadanda ba musulmi ba ne a jihar, inda ya ce mafiya yan lokuta ba sa samun adalci.
Da ya ke maida jawabi Owolabi Salis Ya ce matukar aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar to kuwa zai kafa kwamitin da zai duba yadda za a samar da kotun domin amfanin al’ummar musulmin jihar.