Labaran Kano
Kungiyar ASUU reshen Jami’o’in BUK da Northwest sun gudanar da zanga-zangar lumana

Kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU ta bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su hakkokin su tare da aiwatar da wasu aikace aikace da jami’oin kasar nan ke bukata ko kuma su dauki matakin Tafiya yajin aiki.
Hakan na zuwa ne yayin wata zanga-zangar lumana da shugabanin kungiyoyin suka gabatar a dukkan jami’oin kasar nan.
Freedom Radio ta ziyarci Jami’ar Bayero data North West a nan Kano dan ganin yadda zanga-zangar ta gudana inda taga malaman sun daga kwalaye na nura rashin jin dadinsu kan rashin cika musu alkawurrra da gwamnatin tayi.
You must be logged in to post a comment Login