Kiwon Lafiya
Kungiyar CAGSI ta yi ga majalisar dokokin Kano da ta amince don baiwa matsa damar a faggen siyasa
Kungiyar da ke rajin tabbatar da dai-daito tsakanin jinsi ta jihar Kano wato CAGSI tayi kira ga majalisar dokokin Jihar Kani da ta amince da kudirin da zai baiwa matasa damar shiga faggen siyasa a dama da su a fadin kasar nan.
Shugabar kungiyar Maryam Garba Usman ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai da kuma masu ruwa da tsaki kan tunasar da majalisa dangane da muhimmancin amincewa da kudirin da a turance a ka fi sani da Not too young to rule.
Maryam Garba ta kara da cewa a cikin Jihohin da ake bukatar su yarjewa wannan dokar har yanzu bakwai basu amince da ita ba ciki kuwa har da jihar Kano.
Da yake tsokaci yayin taron Kabiru Sa’idu Dakata cewa yayi suna fata jinkirin sa hannu akan kudirin da yan majalisar Dokokin jihar nan basu yi ba, ya zama alkhairi.
Wakiliyar mu Shamsiyya Farouk Bello ta ruwaito cewa wadanda su kayi bayani a taron sun hada da Muhammad Bello, da Abdulrasaq Alkali, wadanda suke da fatan masu ruwa da tsaki za su yi abinda ya kamata kafin zaben shekarar 2019.