Labarai
Kungiyar direbobin Tirela ta bukaci mahukunta su sanya baki wajen bin jinin mamban su
Kungiyar direbobin manyan motoci shiyyar Kano, ta bukaci hukumomi da su shiga cikin lamarin neman hakkin ran mamban su da ake zargin wani jami’in soja da harbe shi a kan hanyar Kaduna zuwa Kano a karshen makon da ya gabata.
Shugaban kungiyar Alhaji Yusuf Habibu Usman, ne ya bukaci hakan a yau Laraba yayin ziyarar koke da tawagarsu ta kawo tashar Freedom Radio.
A cewar shugaban kungiyar direbobin manyan motocin Alhaji Yusuf Habibu, tun bayan da lamarin ya faru sun tattauna batun da hukomomin tsaro daban – daban, amma da sojoji suka zo sun ba su naira miliyan biyar daga cikin diyyar ran dan uwan nasu.
Haka kuma, ya ce, marigayin ya bar mata daya da ‘ya’ya hudu, kuma duk yaran kanana ne, don haka suke kira ga masu ruwa da tsaki a kan lamarin da su shigo cikin kasancewar kisan gilla da aka yiwa direban.
Ya kara da cewa za su tabbatar da sun bi duk wasu hanyoyin da suka kamata domin ganin sun kwato wa iyalan marigayin hakkinsu.
Alhaji Yusuf Habibu Usman, ya kara da cewa, sun bude hanyar da suka rufe ne sakamakon duba bukatun al’umma da kuma irin halin da masu bin hanyar suka shiga.
Usaini Aminu dan uwa ne ga marigayi Abdulhamid, kuma suna tare da shi a lokacin da lamarin ya faru yana mai cewa, jami’an tsaro ba sa daukar direbobi da muhimmanci inda suke cin zarafinsu akan hanya musamman idan ba su bada cin hanci ba.
Idan dai mai sauraro zai iya tunawa a ranar Larabar data gabata ne aka zargi wani jami’in soja da laifin harbe wani direban mota batare da wani dalili ba, a daidai garin Kunkumi dake kan hanyar Kano zuwa Kaduna wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa nan take.
Wannan lamarai yayi matukar tunzura direbobin manyan motocin wanda hakan yasa suka toshe hanyar baki daya bashiga ba fita har na tsahon kwanaki uku domin dai nemawa dan uwan nasu hakkinsu, wanda kuma daga baya suka sanar da bude ta.
Rahoton: Ummulkhairi Rabi’u Yusuf
You must be logged in to post a comment Login