Labarai
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi Allah-wadai da kisan manoma a Borno
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi All- wadai kan kisan da wasu ‘yan ta’adda su kai wa manoman shinkafa a garin Kwashe dake karamar hukumar Jere ta jihar Borno a ranar Asabar din data gabata.
Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kuma gwamnana jihar Ekiti, Kayode Fayemi da ya fitar a Daren jiya Lahadi.
Sanarwar ta ce kashe manoman shinkafan da a kai su Arba’in da Uku a garin na Jere a matsayin mafi munin harin ta’addanci da akai.
Ta kuma ce Najeriya bazata taba mantawa ba da harin ta’addancin da aka kai garin na Jere.
Sannan kuma sanarwar ta yi kira ga jami’an tsaron Najeriya da su kara gwazo wajen yakin da suke da ‘yan ta’adda.
Kungiyar gwamnonin ta cikin sanarwar ta kuma yi kira ga al’umma da su kara sanya idanu a unguwannin su domin ganin ba’a baiwa ‘yan ta’adda mafaka ba.
You must be logged in to post a comment Login