Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kungiyar NUJ ta yi Allah-wadai da harin bom da aka kai Katsina

Published

on

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Katsina ta yi Allah-wa’adai da harin bom da aka kai ya yi sanadiyar mutuwar yara kanana biyar a jihar Katsina.

NUJ ta kuma yi kira ga gwamantin jihar ta Katsina da ta dauki matakan kare alummar jihar baki daya.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da shugaban kungiyar reshen jihar ta Katsina Tukur Dan-Ali ya sanya wa hannu cewa kamata ya yi gwamnati ta kama tare da gurfanar da wadanda suka aikata hakan.

Kungiyar ta aike da ta’azziyar ta ga gwam,natin jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukar su da mahaifin yaran Alhaji Hussaini Mai-kwai

A dai ranar Asabar ne wani bom ya tashi da kananan yara biyar a kauyen Yammama a karamar hukumar Malumfashi dake jihar ta Katsina.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!