Ƙetare
Hamas da sojojin Isra’ila sun tabbatar da kisan kwamandan rundunar sojin Hamas

Kungiyar Hamas da sojojin Isra’ila sun tabbatar da kisan Izz al-Din Haddad, kwamandan rundunar sojin Hamas da aka fi sani da Qassam Brigades, a wasu hare-hare da Isra’ila ta kai Gaza ranar Juma’a.
Isra’ila ta bayyana shi a matsayin daya daga cikin wadanda suka kitsa hare-haren ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
A lokacin hare-haren da aka kai da daddare an kuma kashe wasu daga cikin iyalan Haddad.
Ƙungiyoyin bayar da agaji a Gaza sun ce akalla mutum bakwai ne suka mutu a lokacin hare-haren, yayain da gommai suka jikkata.
Duk da cewa akwai yarjejeniyar dakatar da wuta tun watan Oktoban bara, gwamnatin Isra’ila na cewa tana da ikon kai hare-hare kan mambobin Hamas.
You must be logged in to post a comment Login