Ƙetare
Iran ta kakkabo wani jirgin yakin Amurka

Rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin yaɓi maras matuki na Amurka ƙirar MQ-1 da ta kai mata hari da shi a safiyar yau
A cikin wata sanarwa da sashen hulda da jama’a na rundunar ya fitar, ta ce jirgin ya yi yunkurin shiga sararin ruwan Iran domin gudanar da ayyukan da ta bayyana a matsayin na tada hankali, amma an gano shi cikin gaggawa tare da harbo shi ta amfani da makamai masu linzami na zamani na rundunar.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce rundunar kariyar sararin samaniyar IRGC ta jaddada cewa yankunan ruwan ƙasar na ƙarƙashin cikakken kulawarta, kuma za ta mayar da martani cikin tsanaki ga duk wani yunƙurin keta huruminta.
Ya zuwa yanzu, rundunar sojojin Amurka (CENTCOM) ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan wannan iƙirari da Iran ta yi ba.
You must be logged in to post a comment Login