Labarai
Kungiyar kwadago NLC ta shirya fara sabon yajin aiki a Kaduna
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ce zata dawo cigaba da yajin aikin da ta dakatar a jihar Kaduna bisa zargin saba yarjejeniya.
NLC ta bayyana hakan ne yayin wani taron gaggawa da shugaban kungiyar Ayuba Wabba ya jagoranta a ranar 22 ga watan Yunin 2021.
Kungiyar ta umarci mabobinta da su sanar da daukacin ma’aikatan jihar tare da wayar musu da kai game da sabon yajin aikin da ake shirin farawa.
Wabba ya zargi gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I da gaza cika ka’idojin yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta kulla tsakanin gwamnatin jihar da NLC.
“Mun yanke shawarar dawowa cigaba da yajin aiki a jihar Kaduna bayan mun aike da takarda ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Ministan kwadago da daukar aiki Chris Ngige,“ inji Wabba.
You must be logged in to post a comment Login