Labarai
kungiyar kwadago ta cimma yarjejeniya da kwamitocin nazarin mafi karancin albashi na gwamnatin tarayya
Shugabannin kungiyar kwadago ta kasa wadanda suka janye yajin aikin da suka yi barazanar farawa a yau Talata, sun cimma wata yarjejeniya kan mafi karancin albashi da kwamitocin nazarin mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta kafa.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, Ayuba Wabba ne ya bayyana haka bayan kammala tattaunawar kungiyar da kwamitin mafi karancin albashi a daren jiya.
Ya ce kwamitocin nazarin mafi karancin albashi sun kammala aikinsu kuma an sanya hannu kan yarjejeniyar da aka cimma.
A cewar Ayuba Wabba, da misalin karfe hudu da kwata na yammacin yau ake saran sanar da sabon mafi karancin albashin, lokacin da za a gabatar da kunshin yarjejeniyar ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Asorok.
Ita ma da ta ke zantawa da manema labarai shugaban kwamitocin nazarin mafi karancin albashin Ms Amma Peple, ta tabbatar da cewa sun amince kan mafi karancin albashin.