Kiwon Lafiya
Kungiyar kwadago ta kasa na nan kan bakanta na tsunduma yajin aikin gama gari
Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta ce har yanzu tana kan bakanta na tsunduma yajin aikin gama gari a ranar 6 ga watan Nuwamban gobe, matukar gwamnatin tarayya ta gaza amincewa da karin mafi karancin albashin Naira dubu talatin ga ma’aikatan Kasar nan.
Sakataren Kungiyar ta Kasa reshen Jihar Kano Kwamared Auwal Mudi Yakasai ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi nan gidan Rediyo Freedom.
Auwal Mudi Yakasai ya ce maganar da mutane suke na cewa matukar aka kara albashi to za’a samu karin hau-hawar farashin kaya a Kasar nan.
Ya kara da cewa suna da hanyoyi guda uku da suke bi wajen neman hakkinsu, amma ta hanyar tafiya yajin aiki ne kawai gwamnati ke saurarensu.
Kwamared Auwal Mudi Yakasai ya jaddada cewa gwamnatin tarayya tana da karfin tattalin arzikin yin karin albashin ma’aikatan ganin yadda farashin gangar Man Fetur ya tashi.