Kiwon Lafiya
Kungiyar Likitoci ta NARD ta yi barazanar tsunduma yajin aiki

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa NARD ta yi barazanar tsunduma yajin aiki sakamakon rashin cika mata alkawuranta da gwamnatin tarayya ta yi.
Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren kungiyar na kasa Dakta Shu’aibu Ibrahim, ya fitar a shafinsa na X.
Ya kuma ce idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, likitocin za su shiga yajin aikin dindindin.
Ta cikin sanarwar ya zargi Ma’aikatar Lafiya ta kasa da gwamnatin tarayya kan watsi da wa’adin aiwatar da yarjejeniyar.
You must be logged in to post a comment Login