Labarai
Kungiyar NATCA ta koka
Kungiyar masu kula da zirga-zirga jiragen sama ta Najeriya, wato Nigerian Air Traffic Association, ta koka gameda rashin isasun kayayyakin aiki tsakanin su da matuka jirage, wanda hakan ke kawo tarnaki ga ayyukan su.
Mataimakin shugaban kungiyar Ahmed Adamu ne, ya bayyana hakan jim kadan bayana kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, wanda ya maida hankali kan yadda kungiyar ke gudanar da ayyukanta.
Ya kara da cewa, kungiyar na kula da jiragen sama tun daga tashi zuwa sauka, domin tabbatar da an samu nasarar tashi da sauka cikin kwanciyar hankali.
A nasa bangaren, daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar, Malam Husaini Jibril ya ce, kungiyar na fuskantar kalubale ta hanyar rashin isassun ma’aikata sakamakon wahalar da dalibai da ke karantar aikin nasu ke fama da shi.
Bakin sun yi kira ga gwamnati kan ta taimaka wajen kawo musu isassun kayayyakin aiki, da daukar nauyin dalibai masu karatun ilimin tukin jiragen sama.