Kiwon Lafiya
Kungiyar NULGE ta bukaci shugaba Buhari ya yi watsi da wasikar kungiyar gwamnoni
Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya NULGE ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da wasikar korafi da kungiyar gwamnoni ta kasa su ka rubuta suna bukatar da a dakatar da shirin bai wa kananan hukumomi ‘yancin sarrafa kudaden su.
Hakan na kunshe ne cikin wata wasika da kungiyar ta NULGE ta rubuta wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, tana kalubalantar korafin gwamnonin kan ‘yancin sarrafa kudade na kananan hukumomin.
A cewar wasikar wadda shugaban kungiyar ta kasa Ibrahim Khaleel ya aikawa shugaban kasa, ta ce, tsarin da sashen kula da hada-hadar kudi NFIU ya fito da shi, zai taimaka gaya wajen kawo karshen almubazzaranci da gwamnoni ke yi da kudaden kananan hukumomin kasar nan dari bakwai da saba’in da hudu.
A baya-bayan nan ne dai kungiyar gwamnoni ta kasa karkashin shugaban ta mai barin gado Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ta rubutawa wasikar korafi ga shugaban kasa tana kalubalantar shirin da sashen kula da hada-hadar kudi ya fito da shi na haramtawa gwamnoni taba kudaden kananan hukumomi farawa daga watan gobe na Yuni.