Kiwon Lafiya
Kungiyar Save the children da Action against hunger sun kaddamar da Shirin tallafawa al’umma a jihohin Kano da Kaduna.
Kungiyar Save the children da hadin gwiwar masu yaki da cutar yunwa wato Action against hunger sun kaddamar da Shirin taimakawa kananan yara domin yaki da rashin isasshen abinci a jihohin Kano da Kaduna.
Da take jawabi lokacin kaddamar da Shirin shugabar Shirin KARINA LOPEZ tace Shirin na Kano da Kaduna ya biyo bayan nasarori da Shirin ya samu a jihohin Jigawa da Zamfara.
shirin na nufin dubawa da taimakon yara a kwanakin su dubu na farko daga lokacin da aka haife su.
Karina Lopez ta Kara da cewa ta hanyar bibiya zaa samu nasarar yaki da cutar tamowa tsakanin kananan yara ta hanyar bayar da tallafi mai karfi a tsakanin iyalai dake fuskantar matsanancin talauci.
A nasa jawabin babban sakatare a maaikatar lafiya ta jahar Kano Alhaji Usman Bala Muhammad yace maganin cutar yunwa tsakanin kananan yara zai taimaka gaya wajen girman su.
Yace Gwamnatin Jahar Kano a shirye take wajen ganin ta taimaki Shirin wajen bayar da nata tallafin domin shiga loko da sako na jahar Kano.
ReplyForward
|