Labarai
Kungiyar tsoffin sojoji tayi alkawarin karbo hakkin mambobin ta
Kungiyar tsoffin sojojin sama dana kasa da ruwa ta kasar nan, wato REMENAF ta sha alwashin karbo hakkin tsoffin sojin da suka bautawa kasar nan hakkunan su musamman ma wadanda suka rasu.
Babban jami’in kungiyar reshen jihar kano Bala Munzali ne, ya bayyana wa tashar Freedom Radio hakan a kan kalubalen da iyalan sojoji suke fuskanta da halin ni ‘ya su da suke shiga bayan kammala aiki.
Bala Munzali ya kara da cewa suna zargin tsohuwar kungiyarsu ta LEGION da gazawa wajen kwatarwa sojojin hakkin su da suka hadar da fansho DA garatuti, hakan ta sa suka kafa wannan kungiya ta REMENAF.
A nasa bangaren shugaban shirin samar da inshorar lafiya sojoji na kasa mai kula da jihohin Kano da Jigawa Tanimu Umar, yace tsarin zai tanadi kyakyawan shirin da zai taimakawa iyalan sojin ba tare da samun tsaiko ko nakasu ba.
Labarai masu alaka.
Rundunar sojin sama ta musanta kai hare-hare kan fararen hula a Zamfara
Jiragen yaki za su iso Najeriya -Rundunar sojan sama
Shi kuwa mataimakin shugaban kungiyar reshen jihar Kano Abdukadir Sulaiman Gwarzo, kokawa yayi kan yadda gwamnati ta gaza basu gudunmawa a matsayin su na wadanda suka hidimtawa kasar nan.
Kungiyar da shuwagabannin ta sun yi kira ga duk wani jami’in soja dake aiki da kuma wadanda suka yi ritaya da su shiga tsarin inshorar lafiya don samun kulawa data dace, kamar yadda wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya ruwaito mana.
You must be logged in to post a comment Login