Kiwon Lafiya
kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje sun gargadin da a guji labarun bogi a lokacin zabe
Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji kitsa labarum bogi da kuma furta kalaman batanci da zai tunzura al’umma wajen tada rikici, kafin da yayin da kuma bayan babban zabe dake tafe.
Wannan na kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa ta bayan taro da kungiyar ta fitar karkashin gamayyar jam’iyyun siyasa na kasar nan da kuma na tarayyar Turai suka fitar
Sanarwar bayan taron ,ao dauke da sa hannun shugaban ta Mr Keneth Gbandi da wakilan jam’iyyu daban-daban da kuma wakilan kungiyoyin kishin al’umma da suka gudanar a can kasar Jamus yayin da suka aikewa kamfanin dilancin labaru na kasa NAN dake Abuja.
Kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kan su wuri guda da wanzar da zaman lafiya ba tare nuna bambacin adani ko siyasa ko kuma aladu ba, ta yadda za’a dakile furta kalaman batanci da kuma tada rikici a cikin al’umma.