Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

CORONA – ‘Yan Najeriya 11 sun mutu a Afrika ta kudu – NASU

Published

on

Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kudancin Afrika (NUSA) ta ce a kalla ‘yan kasar nan goma sha daya ne suka rasu a Afrika ta kudu sakamakon cutar corona.

Shugaban kungiyar Mr Adetola Alubajo ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya fitar a yau Laraba.

Mr Adetola ya kara da cewa, a yanzu suna jiran rahoto daga sauran sassan kasar guda takwas na kididdigar wadanda suka rasu a Afrika ta Kudun.

Sanarwar ta bayyana cewa cutar corona gaskiya ce domin kuwa tayi illa a kasashen duniya da dama, sai dai yace babban kalubalen da suke fuskanta shi ne yadda ‘yan kasar nan da ke Afrika ta kudu suka gaza amincewa da samuwar cutar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, tsangwama da rashin bayyana matsayar lafiyar ‘yan kasar nan da kuma rashin basu agaji, babban kalubale ne da ke illa ga lafitar ‘yan Najeriya mazauna Afrika ta Kudun, duk kuwa da cewa kungiyar ta samar da kayan bada agajin gaggawa.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!