Labarai
Kungiyar ‘yan Sintiri ta Vigilante ta bukaci gwamnatin Kano ta samar da hadin kai tsakanin Kamfanoni masu zaman kansu don samar da Asusun tallafawa jami’an tsaro
Kungiyar ‘yan Sintiri ta Vigilante ta yi kira ga gwamnatin Jihar Kano kan ta samar da hadin kai tsakanin Kamfanoni masu zaman kansu don samar da Asusun tallafawa jami’an tsaron da sauran takwarorinsu na kungiyoyi don inganta ayyukansu a Jihar nan.
Kwamandan kungiyar ta Vigilante a nan Kano Muhammad Kabir Alhaji ne ya yi wannan kira a jiya Lahadi ta cikin shirin Mu Leka Mu Gano na musamman na nan Freedom Rediyo.
Muhammad Kabir Alhaji ya ce akwai bukatar Kamfanonin masu zaman kansu da gwamnati su hada hannu don samar da kayan aiki masu nagarta ga jami’an tsaro kamar yadda ake da irin wannan tsari a wasu Jihohin kasar nan.
Ya kuma kara da cewa kungiyar tana kokarin kaucewa cin zarafin wadanda ta ke kamawa bisa zargin aikata laifi, illa iyaka tana bincike ne tare da mika wadanda ta samu da laifi hannun hukuma don fadada bincike kamar yadda doka ta tanada.
Muhammad Kabir Alhaji ya kuma ce kungiyar Sintirin ta Vigilante na aiki ne da mambobinta na daukacin kananan hukumomin Jihar Kano 44 ba dare ba rana don ganin ta kakkabe ayyukan bata-gari.
Sannan ya kuma bukaci hadin kan daukacin mambobin kungiyar da jami’an tsaro don gudanar da aikin da suka sa a gaba.