Connect with us

Labarai

Kungiyoyin kwadagon Faransa na shirin gudanar da zanga-zangar neman karin albashi

Published

on

Kungiyoyin kwadago a kasar Faransa sun ce za a gudanar da zanga-zanga domin neman karin albashi da kuma nuna adawa da rage kasafin tallafin jin dadi da walwalar al’umma.

 

Hukumomi na sa ran dubban mutane za su halarci gangamin, yayin da ake kokarin shirya babban yajin aikin gama gari a fadin kasar.

 

An dai tura jami’an tsaro da dama domin hana tashe-tashen hankula irin wadanda suka faru a zanga-zangar da aka yi a watan Oktoba na wata jiya.

 

Ana sa ran ma’aikatan gwamnati za su shiga yajin aikin, sai dai har yanzu ba a tabbatar da irin tasirin da hakan zai yi ga harkokin sufuri ba.

 

Kungiyar yellow vest  da kuma kungiyoyin dalibai sun mara wa zanga-zangar baya, bayan sun gudanar da gangami a karshen makonnin baya domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma neman inganta harkar ilimi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!