Connect with us

Labarai

Babbar Kotun Tarayya ta kori Shugabancin ADC tsagin David Mark tare da soke takarar Atiku

Published

on

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, tare da soke dukkan matakan da shugabancin ya ɗauka a madadin jam’iyyar.

Matakan da kotun ta soke sun haɗa da tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen shekarar dubu biyu da ashirin da bakwai.

Jaridar punch ta rawawaito cewa tun da farko, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa sunan Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda har ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.

A hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke ranar Alhamis, kotun ta bayyana kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark a matsayin wanda bai dace da doka ba, tana mai cewa kwamitin ne ya shirya zaɓen fitar da gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta amince da ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar.

Nafiu Bala Gombe ya garzaya kotu ne yana ƙalubalantar yadda kwamitin Sanata David Mark ya karɓi shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Chief Ralph Nwosu, shi ne ya cancanci ya gaje shi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!