Coronavirus
Kusan Mutum dari biyar sun warke da Corona a jihar Kano
Yanzu haka dai mutane 450 ne hukumomi suka tabbatar sun warke daga cutar Corona a Kano.
Ma’aikatar lafiya ta Kano a shafin Twitter ta sanar cewa an samu Karin mutane biyu da suka kamu da cutar a ranar Lahadi, wanda ya kai adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar zuwa 999.
Daga ciki masu dauke da cutar mutum 48 ne suka mutu.
Yanzu haka masu dauke da cutar Covid-19 541 ke cigaba da samun kulawar jami’an lafiya a jihar Kano.
Hari la yau ma’aikatar lafiyar ta ce mutane 5,378 aka yiwa gwajin cutar Coronavirus a jihar Kano.
Wannan na zuwa ne yayinda gwamnatin Kano ta ce ta shirya tsaf domin fara gwajin cutar gida-gida a fadin jihar.
You must be logged in to post a comment Login