Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Har yanzu lockdown na nan a Kaduna – Inji El-Rufa’i

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce har yanzu dokar lockdown na nan, wato dai mutane zasu cigaba da zama a gida suna wanke hannu har zuwa lokacin da gwamnati zata ga dacewar a sassauta dokar.

Gwamna Nasir El-Rufa’I ne ya bayyana hakan a shafin gwamnatin jihar na Twitter da yammacin ranar Lahadi.

Dokar dai na nan har zuwa ranar Talata, wato ranar da wa’adin dokar makon biyu da aka kara za ta kare.

Gwamnatin ta ce kasuwanni da wuraren ibadu da sauransu za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Ranar Talata 9 ga watan Yunin, 2020 ita ce ranar da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i zai gabatarwa da mazauna jihar bayani game da matakan da gwamnati za ta kara dauka a kokarin da take yi na dakile yaduwar cutar Korona Bairos.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!