Labarai
Kuskure ne babba dawowa kwallon kafa yanzu-Gianni Infantino
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA,Gianni Infantino, ya yi kakkausar suka ga shirye shiryen da ake na dawowa kwallon kafa a wasu kasashen ba tare da ‘yan kallo ba.
Gianni Infantino, ya bayyana hakane jim kadan bayan sanarwar da mahukuntan shirya gasar lig ta kasar Jamus (Germany), suka fitar na cewar za’a dawo buga gasar ba ‘yan kallo a watan farkon watan Mayu.
Shugaban na FIFA, yace ‘ba wani wasa da da yafi rayuwar al’umma don haka ya kamata a kara dakatawa tare da jiran ko ta kwana akan yadda Annobar ta Corona, take ciki da matakan da ake dauka don dakile ta’.
Labarai masu alaka.
Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni
Muller ya saka hannu a sabon kwantiragi da Bayern Munich
Infantino, ya ce zuwa yanzu haka sun shaidawa kasashe dari biyu da sha daya, dake cikin hukumar kwallon kafa ta duniya, cewar lafiya itace gaba mafi muhimmanci fiye da komai kuma kowa ya kamata ya san hakan, a yunkurin da hukumar take na kare kowa da kowa.
Don haka zuwa yanzu dawowa buga wata gasa ko kuma yunkuri makamancin haka a wannan hali da duniya take ciki na Annobar da kuma mamayar da take, zai zama rashin hankali ne tsanta.
You must be logged in to post a comment Login