Connect with us

Labarai

‘Yan wasan cikin gida zasu fara wasa a Super Eagles-Shehu Dikko

Published

on

Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF)kuma shugaban hukumar shirya gasar Lig ta kasa LMC, Shehu Dikko,  ya sanar da cewar sabon kwantiragin da hukumar kwallon kafa ta kasa zata baiwa mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Gernot Rohr, zai tabbatar da cewa an baiwa ‘yan wasa masu taka leda a cikin gida damar bada tasu gudunmowar a cikin kungiyar.

Shehu Dikko, ya kara da cewa yanzu haka mai horar wa Gernot Rohr, zaiyi aiki kafada da kafada da mataimakan sa don kallon ‘yan wasan dake buga firimiya ta kasa da duba hazakar su.

Labarai masu alaka.

An fidda alkaluman gasar firimiya ta kasa zuwa wasannin mako na ashirin da biyu

An fitar da sunayen wadan da za a karrama a bangren wasanni

Shehu Dikko, ya ce’ lokaci yayi yanzu haka da za’a takaita laruwa da ‘yan wasa masu buga wasa a kasashen ketare wanda kasar nan tayi shuhura da sunayen su, don haka yanzu za’a bada dama ga ‘yan wasan su nuna hazakar su a kungiyar ta Super Eagles’.

A baya dai hukumar kwallon kafa ta kasa ta sanar da cewar ba zata tsawaita  kwantiragin mai horar wa Gernort Rohr, ba har sai ya aminta da wasu sharudda da hukumar ta gindaya masa, wanda shima a bangaren sa  yace a  shirye yake da karbar sharudan don cigaba da aikin tare da bunkasa harkokin kwallon kafa a  kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!