Kowane Gauta
Kuskure ne Ganduje ya rushewa ‘yan Haji Camp gidaje – Alhajiji Nagoda
Alhajiji Nagoda daga jam’iyyar PDP ya kalubalanci gwamnatin jihar Kano kan batun rushe gidajen mutanan Haji Camp wanda yace hakan da gwamnatin ta Kano ta yi ba karamin kuskure bane.
Alhajiji Nagoda ya bayyana haka ne ta cikin shirin Kowane Gauta na Freedom Radio Kano.
Ya kara da cewa kamata ya yi gwamnatin ta Kano ta nemawa wadannan mutane wani matsugunin amma bata tashesu daga gidajen su da suka jima a ciki ba,
Alhajiji Nagoda yana mai cewa bai dace bayan tashin mutanen a sami wani kuma na nuna cewar abun da gwamnan ya yi, yana kan turba musamman yadda su kaji wani yana marawa lamarin baya.
You must be logged in to post a comment Login