Labarai
Kwalara ta kashe mutane 7 a jihar Zamfara

Wasu bayanai na nuna cewa cutar kwalara ta barke a wasu kananan hukumomin jihar Zamfara inda zuwa yanzu ta hallaka aƙalla mutum bakwai a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum.
BBC ta rawaito cewa Hukumomin sun ce kusan mutum 200 cutar ta kwantar a asibitin kananan hukumomin biyu, tare da gargadin cewa adadin na iya karuwa.
Hon Sulaiman Abubakar Gumi wanda shi ne danmajalisar tarayya da ke wakiltar Gumi/Bukkuyum kuma shugaban kwamitin hukumar raya yankin arewa maso yammaci a majalisar wakilai, ta Najeriya ya sheda wa BBC cewa tun daga ranar 10 ga watan nan na Agusta, 2025 matsalar ta fara inda yanzu take ta karuwa.
Ya ce zuwa yanzu a Bukkuyum kadai an kwantar da mutum wajen 157, tare da fargabar yawan zai iya karuwa da kuma fargabar rasa wasu mutanen a sakamakon cutar.
You must be logged in to post a comment Login