Connect with us

Labarai

Kwalejin Kogi ta dakatar da malamai 7 daga koyarwa

Published

on

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi watau Kogi State Polytechnic ta dakatar da malamai bakwai bisa zargin sayar da handout ba tare da izini ba, baya ga karɓar kuɗi daga ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma zargin neman lalata da ɗalibai mata domin ba su maki.

 

Mai magana da yawun kwalejin, John Onimisi, ya ce malamai shida an dakatar da su ne saboda sayar da handout da littattafai ba tare da izini ba, yayin da aka dakatar da malami ɗaya kan zargin neman lalata da ɗaliba. Ya ce kwamitin ladabtarwa na ci gaba da bincike, kuma za a bayyana sakamakon da zarar an kammala.

 

Wasu ɗaliban kwalejin da suka nemi a sakaye sunan su, sun zargi wasu malamai da neman kuɗi tsakanin N70,000 zuwa N80,000 ko kuma neman lalata da ɗalibai mata domin su samu maki ko kauce wa faɗuwa a jarabawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!